Isa ga babban shafi
Duniya

Merkel ta damu dangane da rikicin kasuwancin China da Amurka

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce, rikicin kasuwancin Amuka da China na shafar duniya baki daya, yayinda ta bayyana fatan magance wannan matsalar a kan lokaci.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban China Xi Jinping
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban China Xi Jinping 路透社
Talla

Uwargida Merkel ta bayyana haka ne a yayin bude zaman tattaunawarta da Firimiyan China, Li Keqiang a birnin Beijing, inda take ziyarar kwanaki biyu.

Mista Li Mai shekaru 63 da haihuwa, Kwararre ne a fannin tattalin arziki,ganawar na a matsayin sako zuwa yan kasuwa da cewa Jamus ta damu ainu da halin da manyan kasashen Amurka da China suka fada a yau.

A cewar Uwargida Angela Merkel tabbas lamarin na daf da kawo rudani ga harakokin cinikaya da kasuwancin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.