Isa ga babban shafi
Hong Kong

Hong Kong ta fasa tasa keyar masu laifi zuwa China

Shugabar Gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam ta ce, za ta janye kudirin dokar tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci bayan matakin ya haddasa mummunar zanga-zangar watanni.

Shugabar Gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam
Shugabar Gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam 路透社
Talla

A cikin watan Afrilu ne aka gabatar da kudirin dokar, yayinda aka dakatar da shi a cikin watan Yuni duk da cewa, uwargida Lam ta ki soke kudirin baki daya.

Janye kudirin dokar, na cikin manyan abubuwa guda biyar da masu zanga-zangar rajin demokradiya ke bukata a yankin na Hong Kong.

A wani jawabi da aka watsa ta kafar talabijin a wannan Laraba, uwargida Lam ta bayyana wasu matakai da aka kirkiro su domin biyan bukatun masu zanga-zangar.

Lam ta ce, wasu manyan jami’an gwamnatinta biyu, za su tsoma baki kan binciken da ake gudanarwa yanzu haka game da tsauraren matakan da jami’an ‘yan sada suka dauka kan masu zanga-zangar.

A ranar Litinin da ta gabata, an jiyo uwargida Lam a wani sakon murya tana zargin kanta da haddasa rikicin siyasa a Hong Kong, tana mai cewa, ba ta cancanci samun afuwa ba saboda wannan tashin hankalin da ta haifar.

Masu zanga-zangar sun shafe tsawon makwanni 14 a jere suna gudanar da gangami, yayinda suka yi arangama da jami’an ‘yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.