Isa ga babban shafi
Amurka- Iran

Za mu katse duk wani shirin kulla yarjejeniya da Amurka -Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya kawar da duk wani yunkuri na tattaunawa da Amurka, inda ya ke cewa kasar sa ba ta da bukatar kulla duk wata nau'in yarjejeniya da Amurka.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani REUTERS/Abdullah Dhiaa Al-Deen
Talla

Yayin jawabi ga Majalisar dokoki, Rouhani ya kuma bayyana shirin kasar na sake rage aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 a cikin kwanaki masu zuwa, muddin tattaunawar da ake yi yanzu haka bata haifar da komai ba nan da ranar alhamis mai zuwa.

Bangarorin biyu dai na fuskantar takun saka ne tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar da Iran ta kulla da kasashen duniya cikin shekarar 2015 kan shirin na hada makamin nukiliya wanda ya samar mata da sauki daga tarin takunkuman da ta ke fuskanta.

Sai dai halartar Mohamed Javad Zarif ministan harkokin wajen Iran taron kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da ya gudana a Faransa ya bude hanyar yiwuwar sasantuwar rikicin bangarorin biyu, bayan da Trump da kansa ya nuna bukatar tattaunawa da Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.