Isa ga babban shafi
Yemen

Farmakin Saudiya ya kashe mutane 100 a Yemen

Sama da mutane 100 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren jiragen sama da rundunar kawancen da Saudiya ke jagoranta ta kaddamar kan cibiyar da mayakan Huthi ke tsare jama’a a Yemen, kamar yadda Kungiyar Agaji ta Kasa da Kasa, Red Cross ta sanar.

Wasu daga cikin gawarwakin mutanen da harin rundunar hadakar Saudiya ya kashe a Yemen
Wasu daga cikin gawarwakin mutanen da harin rundunar hadakar Saudiya ya kashe a Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Rundunar ta ce, ta kai farmakin ne kan sansanin da mayakan Huthi ke amfani da shi wajen adana jiragensu marasa matuka da kuma makamai masu linzami, yayinda ‘yan tawayen na Huthi suka ce, hare-heren sun wargaza ginin da suka mayar da shi kurkuku.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mutane 52 da ake tsare da su a wannan cibiya na cikin wadanda suka gamu da ajalinsu a harin, yayinda 68 suka bace.

Majalisar ta ce, akwai yiwuwar alkaluman mamatan su karu nan gaba, lura da cewa, ana kan gudanar da aikin ceto wadanda buraguzan ginin suka danne.

Kungiyar Red Cross ta garzaya wurin da aka kai farmakin a birnin Dhamar tare da tawagar jami’an kiwon lafiyarta dauke da jakunkunan gawarwaki sama da 100.

Red Cross ta nuna damuwa kan yadda aka kai farmakin kan gidan yarin, tana mai cewa, dokokin kasa da kasa na bayar da kariya ga mutanen da ke garkame a gidajen kaso.

Rikicin Yemen wadda ta kasance kasar Larabawa mafi talauci a duniya, ya lakume rayukan dubban mutane, yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin a matsayin mafi kazancewa da ya fi shafi rayuwar bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.