Isa ga babban shafi
Duniya

Brazil zata Karbi tallafin kudade daga manyan kasashe

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya bayyana cewa zai Karbi tallafin kudade da mayan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya suka ce za su baiwa kasar sa don yaki da iftila’in gobarar daji dake ta bazuwa a yankin Amazon.

Wani yankin dajin Amazon da gobarar daji ta kone a gaf da jihar Rondonia dake kasar Brazil
Wani yankin dajin Amazon da gobarar daji ta kone a gaf da jihar Rondonia dake kasar Brazil © REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Brazil ta bayyana cewa da sharadin, cewa sai takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ya janye kalaman zagin da ya kutuntuma masa.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya Talata, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna goyan baya ga shugaba Bolsonaro na Brazil dangane da kalaman sa game da iftila’in gobarar.

Tun da fari dai wani babban jami’in gwamnatin Brazil ya bayyana cewa kasar bata bukatar tallafin kudi na dala miliyan 20 da kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 ta ce zata bayar don yakar wutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.