Javad Zarif na Iran ya yiwa taron G7 shigar bazata a Faransa
Babban Jami’in Diflomasiyyar Iran kuma ministan harkokin wajen kasar Mohamed Javad Zarif ya yiwa taron G7 can a birnin Biarritz na Faransa shigar bazata, matakin da ke nufin samar da daidaito kan tsamin alakar da ke kara tsami tsakanin Tehran da Amurka.
Wallafawa ranar:
Mohamed Javad Zarif wanda ke fuskantar takunkuman Amurka ya yiwa taron na G7 shigar bazata a jiya Lahadi bisa gayyatar shugaba Emmanuel Macron ko da dai Donald Trump ya ce ya na da cikakkiyar masaniya kan zuwansa, hasalima sai da Macron ya nemi shawararsa kafin aikewa Iran da goron gayyatar.
Gabanin barinsa birnin Biarritz na Faransa, Javad Zarif ya yi tattaunawar akalla sa’o’I 3 da shugaba Emmannuel Macron gabanin komawa Tehran.
Ka zalika yayin jawabinsa gaban wakilan Turai da suka kunshi wakilan kasashen Jamus Birtaniya da kuma Faransa, Javad Zarif ya ce batun tattaunawarsu da Amurka batu ne mai cike da sarkakiya da kuma wahala amma suna bukatar gwadawa.
Sai dai cikin kalaman Donald Trump bayan halartar Zarif Faransa, ya ce lokaci ya yi wuri su fara tattaunawa da Iran yana mai cewa basu matsu a fita daga halin da ake ciki yanzu haka ba.
Shugabannin Turai dai karkashin jagorancin Macron na ci gaba da kai ruwa rana wajen ganin an sulhunta rikicin tsakanin Amurka da Iran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu