Isa ga babban shafi
Brazil

"Da gangan aka haddasa gobarar dake kokarin nakasa dajin Amazon"

Faransa da majalisar dinkin duniya sun bukaci daukar matakan gaggawa domin kare gandun daji mafi girma a duniya wato Amazon, inda kawo yanzu gobara ta kone fadin kasa mai yawan gaske.

Wani yankin dajin Amazon da gobarar daji ta kone a gaf da jihar Rondonia dake kasar Brazil. 21/8/2019.
Wani yankin dajin Amazon da gobarar daji ta kone a gaf da jihar Rondonia dake kasar Brazil. 21/8/2019. REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Jami’an kwana-kwana da masu kula da muhalli sun ce gobarar dajin ta baya bayan nan, ta kone sama da kadada dubu 500 a dajin na Amazon, yayinda kuma gobarar ta kone Karin fadin kasar da ya kai akalla kadada dubu 73 a cikin kasar Brazil.

Sai dai shugaban kasar ta Brazil Jair Bolsorano, ya zargi kungiyoyin dake fafukar kare muhalli da haddasa wannan gobarar domin janyo hankulan kasashen duniya dangane da siyasar gwamnatinsa dake bayar da damar sare gandun daji.

Shugaban na Brazil ya kuma zargi takawaransa na Faransa da nuna halayya irinta ‘yan mulkin mallaka, bayanda shugaba Emmanuel Macron a ranar Alhamis ya bukaci taron kasashen kungiyar G7 ya tattauna kan barnar da gobarar dajin ke tafkawa kan dajin na Amazon, abinda ya bayyana a matsayin babban iftila’i ga kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.