Isa ga babban shafi
Amurka

Gwamnatin Trump ta yi watsi da dokar yaran 'yan gudun hijira

Gwamnatin Amurka ta sanar da shirinta na janye dokar da ke iyankance tsawon lokacin da ya kamata a tsare kananan yaran ‘yan gudun hijira. Wannan dai wani banagare na matakan da gwamnatin Donald Trump ke dauka domin fatattakar ‘yan gudun hijirar da ke shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Nicholas Kamm / AFP
Talla

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gidan Amurka ta bayyana cewa, za ta kawo karshen dokar nan ta shekarar 1997 wadda ta ce, gwamnatin kasar ba ta da hurumin tsare ‘ya’yan ‘yan gudun hijira har sama da kwanaki 20.

Nan da kwanaki 60 ne kasar ta Amurka za ta aiwatar da wata sabuwar doka wacce a wannan karo ba za ta iyakance tsawon lokacin tsare yaran ko kuma iyalansu ba.

Wannan matakin dai, zai share tunanin ‘yan gudun hijira na cewa, za a saki ‘ya’yansu bayan shafe kankanin lokaci a hannun jami’an tsaron kan iyakar kasar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaba Donald Trump ya ce, wajibi ne su yi watsi da wannan doka domin kare yaran ‘yan gudun hijira daga fuskantar cin zarafi da kuma kwarararsu cikin kasar, yana mai cewa, wannan matsala ce da ke bukatar a tunkare ta cikin gaggawa.

Ana dai caccakar gwamnatin Amurka saboda fatali da wannan doka, yayinda ake zargin ta da raba kananan yara da iyayensu, kuma akasarin ‘yan gudun hijirar na fitowa ne daga yankin kasashen tsakiyar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.