Isa ga babban shafi

Amurka ta nemi kara wa'adin takunkuman Iran a Majalisar Dinkin Duniya

Amurka ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kara wa'adin takunkumin karya tattalin arzikin kasar Iran da nufin hana ta mallakar muggan makamai masu linzami da na nukiliya, kiran da ke zuwa dai dai lokacin da wa'adin takunkuman farko ke kokarin karewa a shekara mai zuwa.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo wanda ya gabatar da bukatar gaban zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce barin Iran ta mallaki makaman babbar barazana ce ga zaman lafiyar gabas ta tsakiya.

A cewar Pompeo cikar wa'adin takukuman da kwamitin sulhun ya dibarwa Iran karkashin sashe na 2231 na dokokin Majalisar, na nuni da cewa manyan hafsoshin sojin Iran za su samu zarafin walwala kamar kowa wanda ya ce hakan na da hadarin gaske.

Alaka tsakanin Amurka da Iran dai na kara tsami tun bayan hawan mulkin Donald Trump a shekarar 2016, inda ya fara warware yarjejeniyar da magabacinshi ya kulla da kasar game da shirinta na mallakar makamin nukiliya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.