Isa ga babban shafi
Gibraltar

Jirgin Iran da aka kama a Gibraltar ya kama hanyar Girka

Jirgin dakon man fetur mallakin Iran da Gibraltar ta kama a cikin watan Yuli bisa zargin safarar man fetur zuwa Syria, ya bar tashar jiragen ruwan Gibraltar.

Jirgin ruwan dakon man fetur na Iran da Birtaniya a yankin Gibraltar ta kame cikin watan Yuli.
Jirgin ruwan dakon man fetur na Iran da Birtaniya a yankin Gibraltar ta kame cikin watan Yuli. REUTERS/Jon Nazca/File Photo
Talla

Bayanai sun nuna cewa, tankar ta kama hanyar gabashin tekun Mediterranean da zummar isa Kalamata da ke kasar Girka.

Tun da farko dai, Gibraltar ya yi watsi da bukatar Amurka ta sake kama jirgin na Iran.

A ranar jumm’ar da ta gabata ne, Amurkar ta gabatar da bukatar, kwana guda bayan Gibraltar ta janye umarnin ci gaba da tsare jirgin.

A martanin da ta mayar, Gibraltar tac e, ba za ta iya mutunta bukatar Amurka ba ta sake bayar da umarnin tsare jirgin, tana mai cewa, takunkuman Amurka akan Iran basa aiki a kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.