Epstein mai shekaru 66 wanda kuma ke da alaka da ‘yan siyasa da fitattun mutane a Amurka, ya rataye kansa ne a gidan yarin gyara halinka da ke birnin New York, yayinda aka tsinci gawarsa a safiyar yau Asabar.
A can baya dai, Epstein ya yi kokarin kashe kansa a wannan gidan yari, inda har ya yi wa kansa rauni a wuya.
Gabanin kashe kansa, Epstein na fuskantar barazanar daurin shekaru 45 muddin aka same shi da laifi, yayinda gwamnatin Amurka ta kaddamar da bincike kan mutuwarsa.
Marigayin ya musanta zargin da ake yi masa na sarafarar 'yan mata 'yan kasa da shekaru 18 domin karuwanci a kasaitattun gidajensa da ke Manhattan da Florida a shekarar 2002 da 2005.