Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sha suka a yayin ziyarar jaje a Texas da Ohio

Shugaban Amurka Donald Trump ya jajanta wa iyalai da kuma wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka rutsa da su a jihohin Texas da Ohio, yayinda masu adawa da shi ke ci gaba da sukan sa saboda kalamansa na nuna kyamar baki.

Shugaban Amurka Donald Trump a Dayton na jihar Ohio
Shugaban Amurka Donald Trump a Dayton na jihar Ohio ©REUTERS/Leah Millis
Talla

Shugaba Trump da mai dakinsa Melania sun shafe mafi rinjayen lokacin ziyarar da suka kai wajen janjanta wa wadanda suka jikkata a hare-haren ‘yan bindigar da kuma iyalansu a Dayton da mutane 9 suka halaka, da kuma El Paso da dan bindigar ya yi wa mutane 22 kisan gilla.

Yayin ziyarar, Trump ya fuskanci suka daga al’ummar yankunan da kuma sauran ‘yan adawa da ke zargin sa da karfafa dabi’ar kyamar baki da fifita turawa fararen fata, sakamakon kalaman da shugaban ya sha furtawa masu alaka da batututwa musamman kan bakin-haure ko ‘yan ci rani da ya taba kira da ‘yan mamaya.

Sai dai a lokaci guda, dimbin magoya bayan shugaban na Amurka su ma sun gudanar da nasu gangamin na nuna masa goyon baya.

Ta’addancin da ‘yan bindiga suka yi a bayan-bayan nan a jihohin Texas da Ohio, ya sa sake tayar da muhawara tsakanin masu neman samar da dokokin takaita mallakar bindiga ko ma hanawa da masu adawa da bukatar haka.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da aka yi a watan Mayu, ta nuna cewa kashi 63 daga cikin adadin Amurkawan da aka tuntuba suna goyon bayan haramta mallakar bindiga a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.