Isa ga babban shafi

Za mu kaucewa rige-rigen kera makamai da Rasha- NATO

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya sha alwashin cewa, kungiyar za ta kaucewa shiga gasar rige-rigen kera muggan makamai tsakaninta da kasar Rasha, dai dai lokacin da yarjejeniyar da ke tsakanin Rashan da Amurka ta haramta kera makamai masu linzami da ke cin matsakaicin zango ke kammala rushewa.

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ©REUTERS/Francois Walschaerts
Talla

Yayin gabatar da wani jawabi a Brussels, Jens Stoltenberg ya dora alhakin rushewar yarjejeniyar akan Rasha, wadda ya zarga da ci gaba da kera makaman masu cin matsakaicin zango da ka iya dakon makaman nukiliya.

Ilahirin kasashe 29 na kungiyar tsaron tav NATO ne suka marawa Amurka baya yayin rusa yarjejeniyar ta INF da ta cimma da Rasha a shekarar 1987, wadda ta haramta kera makamai masu linzami da ke tafiyar kilomita 500 zuwa dubu 5 da 500.

Sai dai a shekarun baya bayan nan Amurka ta sha zargin Rasha da kera sabbin makamai masu linzami kirar 9M729 da ke tafiyar matsakaicin zango akalla kilomita dubu 1,500, abinda ya sabawa yarjejeniyar INF, zargin da Rasha ta sha musantawa, inda ta ce makaman da ta kera na yin tafiyar kilomita 480 ne kawai.

Amurka da kungiyar tsaro ta NATO sun ce ire-iren makaman masu linzami da kasar ta Rasha ke kerawa suna da matukar wahalar kakkabowa, kuma za su iya afkawa biranen nahiyar Turai cikin gaggawa, ba tare da samun isasshen lokacin gargadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.