Isa ga babban shafi
Amurka

Biden da Harris sun soki juna a muhawarar Democrat

Mutanen da ke neman ganin Jam’iyyar Democrat ta tsayar da su takarar zaben shugaban kasar shekara mai zuwa sun ci gaba da mahawara a tsakaninsu, inda a wannan karon tsohon mataimakin shugaban kaas Joe Biden da Sanata Kamala Harris suka ci gaba da sukar juna kan manufofinsu.

Joe Biden da Kamala Harris
Joe Biden da Kamala Harris REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Biden ya kaddamar da hari kan abokan takararsa da ke neman Jam’iyyar Democrat ta tsayar da su takarar zaben shugaban kasar shekara mai zuwa, yayinda batutuwa irin su inshorar lafiya da nuna wariyar jinsi da matsalar baki da kuma adalci wajen shari’a suka mamaye mahawarar da suka tafka a cikin daren da ya gabata.

An samu cacar baki tsakanin Biden da Sanata  Harris, fitacciyar bakar fatar da ke cikin 'yan takarar, yayinda suka ci gaba da sukar junan da suka fara a mahawarar farko ta watan jiya.

Masu sa ido sun ce, Biden ke kan gaba cikin 'yan takarar 20 da ke neman samun damar karawa da shugaba Donald Trump a zaben mai zuwa, abinda ya sa daukacin mutanen da ke fafatawa da shi a mahawarar suka ci gaba da mayar da alkiblarsu a kan sa wajen sukar manufofinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.