Isa ga babban shafi
Dubai

Matar Sarkin Dubai na son kotu ta kashe aurenta

Uwargidan Sarkin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, Gimbiya Haya Bint al-Hussein, ta shigar da kara gaban wata kotu a Birtaniya tare da neman abi mata hakkinta kan auren dolen da aka yi mata da sarkin Muhammad bin Rashid Al-Maktoum.

Gimbiya Haya bint Al-Hussein tare da mijinta Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum a Ingila
Gimbiya Haya bint Al-Hussein tare da mijinta Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum a Ingila Reuters
Talla

Gimbiya Haya mai shekaru 45 wadda ta shigar da karar gaban kotun birnin London na bukatar kotun ta kawo karshen aurenta na kusan shekaru 20 da sarkin na Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum, mai shekaru 70 wanda kuma shi ne Firaministan kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

Yayin zaman kotun da ya gudana a ranar Talata, Sarki Mohammed bin Rashid Al-maktoum ya ki bayyana a gaban kotun masarautar birnin na London, inda lauyarsa Helen Ward ta bayyana wa kotu bukatarsa ta ganin an mayar masa da yaransa birnin Dubai.

Haya wadda 'ya ce ga marigayi sarki Hussein na Jordan kuma kanwa ga sarkin kasar na yanzu, sarki Abdallah na II, ta isa kotun ne tare da lauyarta Fiona Shackleton wadda ke kare bukatunta na ganin an bi mata hakki tare da ba ta cikakken iko kan 'ya'yanta.

Karkashin dokar Birtaniya dai, kowacce mace da ke fuskantar auren dole na da damar shigar da kara gaban kotu don bi mata hakki.

Yayin zaman sauraron shari'ar wanda za a ci gaba a ranar Laraba, kotun ta haramta wa wakilan jaridun kasashen ketare shiga kotun, yayinda aka bai wa gidajen rediyo da talabijin na cikin Birtaniya damar zama daga gefen farfajiyar kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.