Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Har yanzu akwai rikicin kasuwanci tsakaninmu da Amurka - EU

Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta ce a shirye take ta kara haraji kan kayayyakin da darajarsu ta kai euro biliyan 35, wadanda Amurka ke kaiwa kasuwanninta, muddin Amurkan ta kara harajin da take caza kan motocinta.

Cecilia Malmstrom, babbar jami'ar lura da sha'anin kasuwancin kungiyar kasashen Turai EU.
Cecilia Malmstrom, babbar jami'ar lura da sha'anin kasuwancin kungiyar kasashen Turai EU. AFP/Sebastien St-Jean
Talla

Babbar jami'ar lura da sha'anin kasuwancin kungiyar kasashen Turan EU, Cecelia Malmstrom ta yi gargadin ne yayin gabatar da jawabi kan sabbin ‘yan majalisun kungiyar ta EU da aka zaba a bana.

Malmstrom wadda ta sanar da dakatarwar tattaunawa tsakaninsu da Amurka don dinke barakar da ta kunno kai kan alakarsu ta kasuwanci, ta tunatar da ‘yan majalisun tarayyar Turan cewa, har yanzu fa rikicin kasuwanci na nan daram tsakaninsu da Amurka, duk da cewa rikicin kasuwancin Amurka da China yafi daukar hankalin duniya.

An dai shafe watanni ana tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da na sauran kasashen Turai don warware takaddamar kasuwancin da ta kai ga shugaba Donald Trump kara harajin kashi 25 da kuma 10 kan karafa da aluminium da kasashen na EU ke shigarwa Amurka.

Har yanzu kuma Trump na nazari kan kara haraji kan ababen hawan da kasashen Turai ke kaiwa Amurka saboda dalilai na tsaro, kamar yadda shugaban ya sha nanatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.