Iran ta musanta harbo jirginta daga Amurka
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif ya ce babu gaskiya cikin ikirarin da Amurka ta yi na harbo wani jirgin leken asirinta maras matuki a mashigin ruwan Hormuz.
Wallafawa ranar:
Javad Zarif ya bayyana haka ne bayan isa zauren majalisar dinkin Duniya don ganawa da babban sakatarenta Antonio Gutterresh.
A jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa dakarun kasar sun harbo jirgin leken asirin na Iran, bayan da ya ketara iyakar da ke tsakaninsu a mashigin ruwan Hormuz.
A makwannin baya Iran ta taba kakkabo irin jirgin leken asirin na Amurka maras matuki, bayan ketara kan iyakarta da tace yayi, zargin da Amurka ta musanta a wancan lokaci,tarkacen jirgin da Iran ta gabatarwa manema labaren kasar ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu