Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/12 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 13/12 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/12 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 13/12 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/12 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/12 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/12 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/12 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/12 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 13/12 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 13/12 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

Faransa da Rasha sun sha alwashin ceto Yarjejeniyar nukiliyar Iran

media Shugaban Rasha Vladimir Putin tareda rakiyar Shugaban Faransa Emmanuel Macron Sputnik/Mikhail Klimentyev/Kremlin via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Rasha Vladmir Putin sun cimma matsayar hada karfi don ceto yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen Duniya daga rushewa.

Matakin ya biyo bayan yadda lamura ke dada zazzafa a yankin gabas ta tsakiya, musamman tsakanin Iran da Amurka.

A jiya alhamis ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaran sa na Rasha Vladmir Poutine suka cimma daidaito don ceto yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen Duniya.

Shugabanin na Faransa da Rasha sun tattauna ta wayar talho tareda jaddada goyan bayan su na ganin an cimma matsalha cikin ruwan sanyi tsakanin Iran da Amurka.

Majiya daga fadar Kremlin daga kasar Rasha na nuni cewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya kira takwaran sa na Rasha, matakin da Vladmir Poutine ya yaba da shi, yayinda Macron ya tsaya kai da fata cewa nauyi ya rataya wuyan kasashen Turai, tareda rakiyar manyan kasashe da suka hada da Rasha da China don tabbatar da yarjejeniyar nukiliya ta shekara ta 2015,tareda yi kira zuwa Iran na ganin ta mutunta alkawuran da ta dau a baya, da kuma zai taimaka don sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Iran.

A farkon watan Yuli ne Iran ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar, tareda daukar alkawarin inganta makamashin nukiliyar ta, Ministan harakokin wajen Jamus Helko Maas a jiya alhamis ya bayana mamakin sa ganin janyewar Amurka daga wannan yarjejeniyar, inda ya kuma yi kira zuwa Iran na ta yiwa Allah ta mutunta wannan yarjejeniya.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure