Isa ga babban shafi
Lafiya-HIV

An samu raguwar mutuwa sanadiyyar HIV Aids a duniya- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu raguwar mutuwa sanadiyyar cutaka masu alaka da HIV a sassan Duniya, sai dai ta yi gargadi kan yadda har yanzu miliyoyin mutane ke rasa damar samun magungunan rage kaifin cutar sanadiyyar karancin tallafin da ake samu a yaki da cutar.

Magungunan rage kaifin cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV Aids wato antiretroviral drugs
Magungunan rage kaifin cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV Aids wato antiretroviral drugs TANG CHHIN Sothy / AFP
Talla

Cikin rahoton shekara-shekara da hukumar UNAIDS mai yaki da cutar ta HIV Aids karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta nuna yadda aka samu mace-mace dubu 770 a bara kasa da na shekarar 2017 da aka samu mace-mace har dubu dari 8 da doriya, haka kuma banbancin akalla kashi 33 da na shekarar 2010 da aka samu mutuwar mutane miliyan 1 da dubu dari 2.

Ka zalika rahoton na Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna takaicinsa kan yadda mutane miliyan 23 da dubu dari 3 kacal ke iya samun magungunan rage kaifin cutar ta HIV wato antiretroviral Therapy cikin fiye da mutane miliyan 37 da dubu dari 9 da ke fama da cutar a sassan Duniya.

Cikin rahoton, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana irin ci gaban da aka samu tun bayan kaddamar da yaki da cutar cikin shekarun 1990, sai dai tace har yanzu akwai karancin agaji a banagaren yaki da cutar.

A cewar daraktar sashen yaki da cutar ta HIV Aids na Majalisar Dinkin Duniya, Gunilla Carlsson, adadin wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar a Afrika yankin da ta fi ta’azzara ya ragu da akalla kashi 5 sai kuma yankin gabas ta tsakiya da kashi 9, ko da dai ta ce ana ci gaba da samun sabbin kamuwa da cutar, wanda ta ce ya fi tsananta a tsakanin masu auren jinsi, fursunoni da kuma karuwai baya ga mashaya.

A cewar Carlsson, tun bayan gano cutar ta HIV Aids cikin shekarun 1980 ta kama akalla mutane miliyan 80 yayinda ta hallaka wasu miliyan 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.