Hukumar ta ce ta gudanar da bincike kan irin wadannan nau’yin abinci har 8,000 daga shaguna sama da 500 da ake sayar da su a kasashen Austria da Bulgaria da Israila da kuma Hungary tsakanin watan Nuwambar shekarar 2017 zuwa Janairun shekarar 2018, kuma sama da kashi 30 na irin wadannan abinci na dauke da zakin da ya wuce kima.
Hukumar ta WHO ta ce duk da ya ke kayan marmari na dauke da nauyin sikari a cikin su, yadda masu sarrafa kayan abincin ke kara sikarin na haifar da matsalar kibar da ta wuce kima da kuma lalacewar hakora.
Daraktan Hukumar a Turai, Zsuzana Jakab ta ce samun abinci mai inganci lokacin yara suna kanana na tasiri wajen rayuwar su.