Isa ga babban shafi

Amurka ta musanta sanya ranar janye dakarunta daga Afghanistan

Jakadun Amurka da ke halartar taron tattaunawa kasar da shugabancin kungiyar Taliban, sun musanta batun cewa Washington ta sanya ranar kammala kwashe sojinta dubu 14 da ke yaki a Afghanistan.

Taron wakilan Amurka da na Taliban a birnin Doha na Qatar
Taron wakilan Amurka da na Taliban a birnin Doha na Qatar Qatari Foreign Ministry/Handout via REUTERS
Talla

Zalmay Khalizad babban jakadan Amurka a tattaunawar, y ace babu shakka ana samun gagarumin ci gaba kuma Taliban a shirye ta ke ta ajje makamai, sai dai har yanzu ba a kai bigiren da Amurkan za ta sanar da lokacin da za ta kammala janye dakarun ba.

Ko cikin watan jiya, sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo yayin ziyarar da ya kai Afghanistan ya bayyana cewa a shirye su ke su kammala cimma yarjejeniyar fahimtar juna tare da daura aniyar janye dakarun kafin nan da watan Satumba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.