Amurka ta musanta sanya ranar janye dakarunta daga Afghanistan
Jakadun Amurka da ke halartar taron tattaunawa kasar da shugabancin kungiyar Taliban, sun musanta batun cewa Washington ta sanya ranar kammala kwashe sojinta dubu 14 da ke yaki a Afghanistan.
Wallafawa ranar:
Zalmay Khalizad babban jakadan Amurka a tattaunawar, y ace babu shakka ana samun gagarumin ci gaba kuma Taliban a shirye ta ke ta ajje makamai, sai dai har yanzu ba a kai bigiren da Amurkan za ta sanar da lokacin da za ta kammala janye dakarun ba.
Ko cikin watan jiya, sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo yayin ziyarar da ya kai Afghanistan ya bayyana cewa a shirye su ke su kammala cimma yarjejeniyar fahimtar juna tare da daura aniyar janye dakarun kafin nan da watan Satumba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu