Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Geng Shuang ya bayyana matakin na Trump a matsayin abin takaici.
Shi dai Trump ya bayyana cewar masu neman dimokiradiya ne ke zanga-zangar, amma wasu gwamnatoci basa bukatar dimokiradiyar.
A yayin wani jawabi da ta gabatar, jagorar gwamnatin Hong Kong Carrie Lam ta yi bayyana cewa, "Amfani da karfi wajen tashin hankali da kuma lalata kayan gwamnati da masu zanga-zanga suka yi, bayan sun kutsa kai cikin ginin majalisar, wani abu ne da ya dace mu yi tir da shi saboda babu abinda ke da muhimmanci da ya wuce mutunta doka da oda a Hong Kong. Saboda haka ina fatar cewar al’ummomi da dama za su amince da mu cewar, wannan tashin hankalin da muka gani, ya zama wajibi mu yi tir da shi."
Zanga-zangar Hong Kong ta samo asali ne bayan gwamnatin yankin ta bayyana shirinta na tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci a can, lamarin da al'ummar yankin suka ki amincewa da shi.