Isa ga babban shafi

Amurka da China sun dakatar da yakin kasuwanci tsakaninsu

Shugaban Amurka Donald Trump, da takwaransa na China Xi Jingpin, sun cimma yarjejeniyar dakatar da yakin kasuwancin da ke tsakaninsu, tare da bayyana cewa wakilan kasashen 2 za su cigaba da ganawa don kawo karshen takaddamar.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping a birnin Osaka na Japan.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping a birnin Osaka na Japan. AFP Photo/Brendan Smialowski
Talla

Bayan ganawarsu a birnin Osaka na Japan inda aka kammala taron kasashen G20, Trump yayi alkawarin dakatar da shirinsa na dora haraji kan Karin wasu kayayyakin da China ke shigarwa Amurka da darajarsu takai dala biliyan 350.

Babu dai Karin bayani kan sauran batutuwan da shugaban na Amurka da China suka tattauna akai.

Yau asabar ne kuma shugaba Trump ya isa Korea ta Kudu, gabannin ziyarar da yake shirin kaiwa Korea ta Arewa don sake ganawa da takwaransa Kim Jong-un.

Gobe lahadi 30 ga watan Yuni, Trump zai tattauna da shugaba Kim, kan shirin nukiliyar kasar da Amurka ta dade tana neman Korea ta Arewa tayi watsi da shi.

Karo na uku kenan da shugabannin biyu za su tattuna, bayan ganawar da suka yi sau biyu a Singapore da kuma Vietnam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.