Isa ga babban shafi

Falasdinawa sun kalubalanci taron Bahrain da Amurka ke Jagoranta

Al’ummar Falestinawa sun soki taron sasanta rikicin gabas ta tsakiya da Amurka ke jagoranta a Bahrain da zimmar kaddamar da wani asusun bunkasa tattalin arzikin Isra'ila da yankin na Falasdinu ta hanyar zuba jarin Dala biliyan 50.

Jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas
Jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

Jiga-jigan masu harkan mai da ke Amurka, da kasashen Larabawa masu arzikin man fetur da cibiyoyin duniya ne ke halartan taron na Bahrain, wanda mahalarta musamman Isra'ila ke halarta ba don komi face saboda rashin dasawarta da Iran.

Isra'ila dai na fuskantar haramcin halartan duk wani taron kasashen Larabawa ne face da takaddar shaidar wata kasa, haka zalika 'yan jaridunta.

Wasu kadan daga cikin ‘yan Jaridu daga Isra'ila ke halartan wannan taro a Bahrain, wanda hakan saboda Amurka na ciki ne tsundum, kuma ya kasance karon farko da aka bar ‘yan jaridun Israela tsoma kafa a Bahrain.

Jason Greenblatt mashawarcin Shugaba Donald Trump na Amurka wanda ya ke daya daga cikin jiga-jigan da suka shirya taron ya bayyana cewa kasar Bahrain na sahun gaba wajen ganin an sami zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.