Mutane 24 sun mutu a rubtawar gini a Cambodia
Akalla mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon rubtawar wani ginin bene mai hawa bakwai a Cambodia, yayinda masu aikin agaji ke ci gaba da kokarin zakulo wadanda buraguzai suka binne duk da cewa, ana kyautata zaton babu mai sauran numfashi.
Wallafawa ranar:
Rahotanni na cewa, benen da ba a kammala gininsa ba, ya rubta ne a daidai lokacin da ma’aikatan ginin da iyalansu ke barci a cikin sa.
Ana yawan samun matsalar rushewar gine-gine a Cambodia, kasar da ta yi fice wajen rashin daukan tsauraren matakai kan masu karya dokokin gine-gine.
Sai dai a wannan karo an cafke mutanen China guda uku da ke kula da ginin, kuma a halin yanzu ana kan gudanar da bincike.
Firaministan kasar, Hun Sen ya ziyarci inda ibtila’in ya faru a yankin Sihanoukville dake kusa da gabar teku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu