Isa ga babban shafi
FAO-china

A karon farko an zabi dan China a matsayin shugaban FAO

A karon fako, an zabi dan asalin kasar China, Qu Dongyu a matsyin sabon shugaban Hukumar Samar da Abinci da Bunkasa Ayyukan Gona ta Majalisar Dinkin Duniya bayan ya samu kuri’u 108.

Sabon shugaban Hukumar Samar da Abinci da Bunkasa Ayyukan Gona, Qu Dongyu.
Sabon shugaban Hukumar Samar da Abinci da Bunkasa Ayyukan Gona, Qu Dongyu. Vincenzo PINTO/AFP
Talla

Mr. Qu mai shekaru 55, ya doke Catherine Geslain Laneele ta Faransa da ta samu kuri’u 71, da kuma Davit Kirvalidze na Georgia wanda ya samu kuri’u 12.

Mr. Qu kwararre ne a fannin ilimin halittu da tsirrai, kuma ya dare ne kan kujerar shugabnacin hukumar a daidai lokacin da ake samun kalubalen kawar da yunwa a duniya saboda matsalar dumamar yanayi da yake-yake.

A cikin shekaru uku da suka gabata, matsalar yunwa ta ta’azzara a duniya musamman a nahiyar Afrika da yankin Gabas ta Tsakiya, abinda ke nuna cewa, akwai tarin kalubale a gaban sabon shugaban na Hukumar FAO.

Hukumar ta bayyana damuwarta kan barazanar karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki, yayinda ake ganin dole ne Mr. Qu ya tashi tsaye wajen gaggauta agaza wa kananan manoma da masu sana’ar kamun kifi domin magance asarar albarkatun gona da talauci.

Mr. Qu wanda ya gaji Jose Graziano da Silva na Brazil, dole ne ya fara samar da tsare-tsaren ciyar da mutanen duniya da aka ce, adadinsu zai kai biliyan 9.7 daga biliyan 7.7 nan da shekarar 2050.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.