Isa ga babban shafi
Turkiya

Jam'iyyar Erdogan ta sha kashi a zaben birnin Santanbul

Jam’iyyar shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ta sha kaye a zaben Magajin Garin Birnin Santanbul da aka sake gudanarwa, abinda ake kallo a matsayin babban koma-baya ga jam’iyyar wadda ta shafe shekaru 25 tana mulkin birnin na Santanbul.

Ekrem Imamoglu na jam'iyyar adawa da ya lashe zaben Magajin Garin Santanbul
Ekrem Imamoglu na jam'iyyar adawa da ya lashe zaben Magajin Garin Santanbul REUTERS/Huseyin Aldemir
Talla

An kidaya kusan daukacin kuri’un da aka kada, inda sakamakon ke nuna cewa, dan takarar jam’iyyar adawa Ekrem Imamoglu na jan ragama da sama da kuri’u dubu 775, kwatankwacin kashi 54 na kuri’un, yayinda abokin karawarsa na jam'iyya mai mulki, Binal Yildrim ke da kashi 45.

Kuri’un da Imamoglu ya samu a wannan karo, sun kara yawa sosai idan aka kwatanta da wanda ya samu a zaben farko da aka soke, inda ya bai wa Yildrim ratar kuri’u akalla dubu 13.

An soke zaben farko da aka gudanar a cikin watan Maris da ya gabata bayan jam’iyyar AKP mai mulki ta ce, an tafka kura-kuren zabe.

Tuni shugaba Erdogan ya aika da sakon taya murna ga Imamoglu, yayinda shi kuma ya bayyana aniyarsa ta aiki tari da shugaban kasar.

A can baya, shugaba Erdogan ya ce, duk wanda ya lashe birnin Santanbula, tamkar ya lashe kasar Turkiya ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.