Isa ga babban shafi
Iran

Amurka za ta dandana kudarta idan ta kai mana hari - Iran

Iran ta yi gargadin cewa Amurka za ta dandana kudarta muddin ta kuskura ta kai mata hari, kamar yadda a baya bayan nan ta so aikatawa.

Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Amir Hatami.
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Amir Hatami. REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Iran tace idan har Amurkan ta aikata wannan ganaganci to tamkar ta yamutsa duka wadansu muradunta ne da ke yankin gabas ta tsakiya da kuma tare da jefa kawayenta cikin zulumin fuskantar hare-haren ramuwa.

Gargadin na Iran ya zo ne bayan da a jiya Juma’a, shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa, ya bada umarnin janye aniyar kaiwa Iran hari, mintuna 10 kafin zartas da umarni.

Farmakin da Amurka ta so kaiwa, martani ne kan harbo mata jirgin liken asiri da Iran ta yi, bayan da ta ce jirgin mara matuki ya ketara kan iyakarta ta ruwa.

A cikin watannan dai dagantaka ta kara yin tsami tsakanin Iran da Amurka bayan harin da aka kaiwa wasu jiragen ruwa maso dakon danyen mai a mashigin tekun Oman, wanda Amurka ta dora alhakin harin kan Iran.

Sai dai a baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin zama babban aboki ga kasar Iran, muddin ta yi watsi da baki dayan shirinta na nukiliya.

Kalaman na Trump sun zo ne kasa da awanni 48, bayan umarnin kaiwa Iran din hari da yayi da nufin maidamartani kan harbor jirgin liken asirin kasar da ta yi, harin da daga bisani Trump din ya dakatar mintuna 10 kafin aiwatar da umarnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.