Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Kiris ya rage sojojin Amurka su kai wa Iran hari

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince wa sojojin kasar da su kaddamar da harin martani kan Iran kafin daga bisani ya soke umarnin kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka rawaito.

Jirgin saman Amurka mara matuki na shawagi a sararin samaniya
Jirgin saman Amurka mara matuki na shawagi a sararin samaniya REUTERS
Talla

Jaridar New York Times ta rawaito daga wasu manyan jami’an fadar White House cewa, an shirya kaddamar da hare-haren akan wasu tsirarun wurare a Iran da suka hada da na’urar hangen jiragen sama da kuma batiran makaman nukiliyar kasar ta Iran .

Jami’an na fadar White House sun ce, sojojin Amurka na gab da kai farmakin kafin shugaba Trump ya dakatar da su, amma kawo yanzu fadar ta White House ba ta ce uffam ba kan batun harin martanin.

Wannan dai na zuwa ne bayan Iran ta harbo jirgin Amurka mara matuki da ke shawagin leken asiri, abinda Trump ya bayyana a matsayin babban kusukuren da Iran ta tafka.

Kasar Iran ta ce, jirgin ya keta sararin samaniyarta a sanyin safiyar ranar Alhamis, yayinda Amurka ke cewa, an harbo jirgin ne a sararin samaniyar kasa da kasa.

Ana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakanmin kasashen biyu a ‘yan kwanakin nan, inda a baya-bayan nan, Amurka ta zargi Iran da kai hari kan tankokin dakon mai a yankin tekun Gulf.

Kazalika Iran ta ce, nan kusa za ta zarce iyakarta da kasashen duniya suka gindaya mata a shirinta na makamin nukiliya, matakin da ke zuwa bayan Amurka ta fice daga yarjejeniyar da aka cimma da Iran a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.