Isa ga babban shafi
Amurka-Trump

Trump ya kaddamar da yakin neman zaben 2020

Shugaba Donald Trump na Amurka ya kaddamar da yakin neman zabensa daga birnin Orlando na jihar Florida, inda ya ke shirin tsayawa takarar neman shugabancin kasar karo na biyu a zaben da za a yi a shekara ta 2020.

Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da ya ke kaddamar da yakin neman zabensa a birnin Orlando na jihar Florida
Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da ya ke kaddamar da yakin neman zabensa a birnin Orlando na jihar Florida REUTERS/Carlos Barria
Talla

A gaban magayo bayansa kusan dubu 20 ne Donald Trump ya kaddamar da yakin neman zaben, inda yake cewa zai ci gaba da tabbatar da Amurka a matsayin kasa jagora kuma mai fada a ji a siyasa da kuma tattalin arzikin duniya.

Trump ya ambaci irin nasarorin da ya ce ya samu sakamakon siyasar hana baki shiga Amurka, tare da kokarin kare masana’antun kasar daga abin da ya kira mamayar takwarorinsu na kasashen ketare.

Daga nan ne kuma Donald Trump wanda aka zaba a matsayin shugaban Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Republican a shekara ta 2016, kamar dai yadda ya saba a irin wannan yanayi, ya yi dirar mikiya da kuma kakkausar suka a kan kafafen yada labarai wadanda ya zarga da sharara bayanan karya a game da shi, kafin daga bisani ya yi suka ga wanda ya gabace shi Barack Obama, da kuma tsohuwar sakatariyar wajen Amurka Hillary Cliton.

Har ila yau Trump ya fito fili karara inda ya yi fatali da binciken Robert Mueller dangane da zargin shisshigin Rasha a zaben da ya ba shi nasara a shekara a 2016, inda ya ce wasu ‘yan siyasa ne suka so yin amfani da wannan batu don shafa masa kashin kaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.