Isa ga babban shafi
Saudiya-MDD

Bincike ya gano hannun Yariman Saudiya a kisan Kashoggi

Wata babbar jami’ar hukumar kare hakkin dan adama ta Majalisar Dinkin Duniya mai zaman kanta Agnes Callamard, ta yi ikirarin cewa sun samo kwararn hujjoji da ke nuna hannun Yariman Saudiya mai jiran gado Muhammad bin Salman a kisan dan jaridar kasar da ke zama a Turkiya Jamal Khashoggi.

Fitaccen dan jaridar Saudiya mazaunin Turkiya, Jamal Khashoggi
Fitaccen dan jaridar Saudiya mazaunin Turkiya, Jamal Khashoggi DR
Talla

Agnes Callamard wadda ta bukaci binciken kasa da kasa, ta ce binciken da suka samu ta hannun daidaikun mutane da ke da hannu a kisan ya nuna cewa sun aikata shi ne bisa umarnin Yariman.

Cikin rahoton da na Agnes Callamard da ta fitar yau Laraba ta bukaci, sanya takunkumai kan Yariman har zuwa lokacin da za a samu hakikanin wadanda suka kitsa kisan dan jaridar.

A cewar rahoton na Callamard, akwai bayanai da ke nuna yadda Khashoggi da kansa ke tsoron iko da izzar yariman na Saudiya matakin da ya sanya shi a tsoranshi a batutuwa da dama.

A ranar 2 ga watan Oktoban bara ne aka yiwa fitaccen dan jaridar Saudiyar mazaunin Turkiya Jamal Khashoggi kisan gilla a Ofishin jakadancin Saudiyan na birnin Santanbul.

Kafin rasuwarsa dai Khashoggi ya yi kaurin suna wajen caccakar manufofi da siyasar Yarima mai jiran gado na Saudiyar Muhammad Bin Salman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.