Isa ga babban shafi
Ghana

Jami'an tsaro sun ceto 'yan Canadan da aka sace a Ghana

Jami’an tsaron Ghana sun yi nasarar kubutar da ‘yan mata biyu, ‘yan kasar Canada da wasu ‘yan bindiga suka  sace a birnin Kumasi a makon da ya gabata.

Jami'an 'yan sandan Ghana
Jami'an 'yan sandan Ghana alternativeafrica
Talla

An dai sace ‘yan matan ne masu shekaru 19 da 20 ranar 4 ga watan Yunin da muke ciki, yayinda suke cikin motar tasi don isa ga sabgoginsu, suna isa wani kulob din masu kwallon lambu ne kuma, 'yan bindigan suka yi awon gaba da su.

'Yan sandan Ghana sun ce, 'yan matan na aiki ne da wata kungiyar tallafa wa matasa mallakin kasar Canada, mai shalkwata a birnin Toronto.

Ba kasafai aka saba satar mutane tare da yin garkuwa da su a Ghana ba, matsalar da a baya bayan nan ke karuwa, la’akari da cewa a shekarar bara aka sace wasu mata ‘yan asalin kasar a kudancin tashar ruwan Takoradi.

Kazalika a watan Afrilun da ya gabata, an sace wani dan kasar India a birnin Kumasi, wanda aka nemi makudan kudade kafin sakin sa, sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo ba jami’an tsaron kasar suka yi nasarar ceto shi.

Wata kdiddiga ta nuna cewa, a duk shekara sama da ‘yan kasashen ketare miliyan daya da dubu 300 ne ke ziyartar kasar Ghana, akasarinsu domin yawan shakatawa da kuma kasuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.