Isa ga babban shafi
Nijar

Nakiya ta tarwatsa tankar yakin Amurka a Nijar

Wata tankar yakin Amurka ta tarwatse bayan taka nakiya a yammacin Jamhuriyar Nijar, kamar yadda jami’an tsaron kasar da kuma ofishin jakadancin Amurka suka tabbatar.

Mayakan Jihadi sun kashe sojojin Amurka 4 a shekarar 2017 a Nijar
Mayakan Jihadi sun kashe sojojin Amurka 4 a shekarar 2017 a Nijar AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE
Talla

Hukumomin tsaron sun ce ba a samu hasarar rai a harin ba, illa tankar yakin da ta lalace, sai dai an kaddamar da bincike don gano ko an dasa nakiyar ce da gangan don kai wa dakarun na Amurka farmaki.

Majiyoyin tsaro sun ce, lamarin ya auku ne a Ouallam da ke yankin Tillaberi a gaf da kan iyakar kasar ta Nijar da Mali, yankin da a shekarar 2017, mayaka masu da’awar jihadi suka hallaka sojojin Nijar 5 da kuma takwarorinsu na Amurka 4.

Yankin na Ouallam mai nisan kilomita 100 daga birnin Yamai, wuri ne da ke zama mazaunin sansani mafi girma da ake horas da sojojin Nijar, domin tura su aiki a karkashin rundunar Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA da ke aikin samar da tsaro a kasar Mali.

A ranar 14 ga watan Mayun da ya gabata, wasu mayaka da ke da’awar jihadi sun hallaka sojojin Jamhuriyar Nijar 28 a gaf da kauyen Tongo Tongo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.