Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta karbi 'ya'yan mayakan jihadi na Syria

Gwamnatin Faransa ta karbi wasu kananan yara marayu da aka kashe iyayensu bayan sun yi balaguro zuwa Syria domin shiga cikin kungiyar mayakan jihadi. Hukumomin Kurdawa ne suka mika marayun bayan gwamnatin Faransa ta bukaci haka.

Daya daga cikin sansanonin kula da iyalan mayakan jihadin Syria da suka zo daga kasashen ketare.
Daya daga cikin sansanonin kula da iyalan mayakan jihadin Syria da suka zo daga kasashen ketare. REUTERS/Ali Hashisho
Talla

Kananan yaran da adadinsu ya kai 12, sun yi rayuwa ne a sansanonin da aka jibge iyalan mayakan jihadin Syria ‘yan kasashen waje bayan fatattakar su daga tungarsu ta karshe.

Hukumomin Kurdawa ne ke kula da sansanonin mai dauke da kananan yara da mata da ke da nasaba da mayakan jihadin Syria da suka zo daga kasashen ketare.

Babban mai kula da harkokin wajen Kurdawa, AbdelKarim Omar ya bayyana cewa, an mika yaran ne a garin Ain Issa da ke kusa da kan iyakar kasar Turkiya a jiya Lahadi, yayinda a gefe guda aka kuma mika wasu yara marayu biyu ga gwamnatin Netherlands.

Ko a makon da ya gabgata, sai da aka mayar da wasu mata Amurkawa biyu da kananan yara shida da ake zargin mayakan jihadi ne zuwa Amurka.

A ranar 23 ga watan Maris ne, rundunar SDF da ta kunshi mayakan Kurdawa da Larabawa ta sanar da wargaza daular kungiyar ISIS bayan rundunar hadaka ta kasashen waje karkashin jagorancin Amurka ta taimaka wajen ganin bayan kungiyar mai ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.