Isa ga babban shafi
Duniya

Ana zaben Shugaban kasar Kazakhstan

A yau lahadi mutan kasar Kazakhstan ke zaben shugaban kasa bayan da Shugaban kasar mai ci Noursoultan Nazarbaiev ya yi murabis a watan Maris sanadiyar rashin lafiya.

Kassym-Jomart Tokayev daya daga cikin yan takara dake rike da shugabancin rikon kwariya na kasar
Kassym-Jomart Tokayev daya daga cikin yan takara dake rike da shugabancin rikon kwariya na kasar Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS
Talla

Akalla mutane milyan 10 ne hukumar zaben kasar ta bayyana su a matsayin wanda suka yi rijista, sai dai ana hasashen daya daga cikin mukaraban Noursoultan Nazarbaiev kuma shugaban rikon kwariya Kassym Jomart Tokaiev lashe wannan zabe.

Kassym Jomart Tokaiev mai shekaru 66 zai fafata da wasu yan takara guda shida,yan takaran da basu da wata kima a idanu yan kasar ta Kazakhstan.

Kazakhstan na daga cikin tsofin kasashen daga tarrayar Soviet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.