Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela ta bude kan iyakar kasar da Colombia

Bayan share watanni ana gudanar da zanga-zanga a Venezuela ,Shugaban kasar Nicolas Maduro ya umurci a sake bude kan iyakar kasar da Colombia a yankin Tachira dake yammacin kasar. 

Kan iyaka da ta hada Venezuela da Colombia
Kan iyaka da ta hada Venezuela da Colombia IOMEcuador
Talla

A watan Fabrairu bana ne Shugaban kasar ya dau mataki na rufe ga baki daya kan iyakokin kasar na sama ,na ruwa da na kasa da wasu tsibirai dake raba iyaka da kasar sa, biyo bayan rikicin siyasa da ya kuno kai tun bayan da Juan Gaido ya ayana kan sa a matsayin Shugaban kasar ,lamarin da ya haifar da tarzoma a kasar.

Kasashen Duniya na ci gaba da kira zuwa yan siyasar Venezuela don gani sun cimma matsaya ta gari da nufin dawo da doka da oda,yayinda wasu rahotanni ke nuni cewa kusan mutane milyan daya ne suka gudu daga kasar zuwa wasu kasashe sabili da rashin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.