Isa ga babban shafi
Duniya

Rasha ta janye daga yarjejeniyar daina kera makaman nukiliya

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce kasar ta kammala janyewa baki daya daga yarjejeniyar daina kera makaman nukiliya da ta kulla tun shekarar 1987 tsakaninta da Amurka.

Vladmir Poutine Shugaban kasar Rasha
Vladmir Poutine Shugaban kasar Rasha 路透社。
Talla

Shugaban Rasha,Vladmir Poutine ya yi gargadin cewa rashin yarjejeniyar zai iya kasancewa bala’i ga Duniya.

Putin wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha gabanin taron tattalin arziki na duniya, ya ce Rasha na a shirye domin tattaunawa tare da samar da sabuwar yarjejeniya bayan rugujewar wadda aka kulla a shekara ta 1987 saboda zaman lafiyar duniya.

A watan oktoban shekarar 2017 ne Amurka ta ce, ba ta da niyyar sanya hannu kan yarjejeniyar haramta mallakar makamin nukiliya wadda ta samu goyon bayan kasashen duniya 122 a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar Amurka, yarjejeniyar ba za ta taka wata muhimmiyar rawa ba wajen tabbatar da zaman lafiya ko kuma inganta sha’anin tsaro a duniya.

Ma’aikatar Harakokin wajen kasar ta Amurka ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, kasashen Duniya da suka mallaki makamin ba su goyi bayan yarjejeniyar ba.

Kasashen da suka mallaki nukiliya sun hada da Amurka da Rasha da Faransa da Birtaniya da China da India da Pakistan da Isra’ila da kuma Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.