Isa ga babban shafi
Amurka-Mexico

Trump ya lafta wa kasar Mexico sabon haraji

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasar za ta dora harajin kashi 5% kan duk wasu kayayyakin da ke fitowa daga kasar Mexico har sai zuwa lokacin da bakin haure suka daina tsallaka iyakar Mexico domin shiga Amurka.

Donald Trump a Washington, ranar 17 ga watan mayun 2019.
Donald Trump a Washington, ranar 17 ga watan mayun 2019. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Shugaba Trump ya sanar da wannan shiri ne ta hanyar da ya saba aikewa da sako wato kafar twitter, inda yake cewa daga ranar 10 ga watan Yuni mai zuwa, Amurka za ta dora wa Mexico karin kashi 5 na kudin fiton kayan da take kai wa kasar, har sai zuwa lokacin da bakin haure suka daina shiga kasar.

Trump ya ce za’a ci gaba da kara harajin har sai an tabbatar da cewar an shawo kan matsalar kafin a janye shi.

Karin hasken da fadar shugaban ta yi ya ce daga ranar 1 ga watan Yuli kudin fito zai tashi zuwa kashi 10, kana za’a dinga kara kashi 5 kowanne wata har sai ya kai kashi 25 nan da ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

A wasikar da ya rubuta masa bayan wannan sanarwa, shugaban kasar Mexico Andres Lopez Obrador, ya bukaci tattaunawa, inda ya ce ba a bukatar yin fito na fito tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.