Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Brazil iya tsawon rayuwarsa

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta tabbatar da dakatarwar da ta yi wa shugaban hukumar kwallon kafa na Brazil, Marco Del Nero har iya tsawon rayuwarsa a wata sanarwa da ta fitar, a Litinin.

Le président de la FIFA Gianni Infantino à Calcutta le 27 octobre 2017
Le président de la FIFA Gianni Infantino à Calcutta le 27 octobre 2017 REUTERS/Rupak De Chowdhuri
Talla

A watan Afrilun shekarar da ta gabata kwamitin ladaftarwar FIFA ta haramta wa Marco Del Nero shiga duk wata sabga da ta shafi kwallon kafa har abada.

Bayan daukaka kara a hukumar daukaka kara, takunkumin da ya taho da tarar Yuro dubu 889 ya tabbata.

Kotun da ke kula da duk wani abinda ya shafi badakala ta FIFA ce ta hukumta Del Nero dangane da laifin karbar rasahawa daga kamfanonin da ke daukar nauyin wasanni a kudancin Amurka.

Del Nero mai shekaru 78, wanda lauya ne, ya gaji Jose Maria Marin, wanda shi ma wata kotu Amurka ta daure shi shekaru 4 a gidan yari sakamakon rashwa, a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Brazil a shekarar 2015.

Yanzu Rogerio Caboclo, tsohon na hannun damar Del Nero ne ke jan ragamar shugabancin hukumar kwallon kafar Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.