Isa ga babban shafi
Venezuela

Fursunoni 25 sun mutu a rikicin gidan yarin Venezuela

Akalla fursunoni 25 sun rasa rayukansu, yayinda jami’an ‘yan sanda 20 suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke a wani gidan yari da ke kudancin kasar Venezuela.

Ana yawan samun rikici a gidajen yarin Venezuela
Ana yawan samun rikici a gidajen yarin Venezuela REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

An samu tashin hankalin ne bayan wasu jami’an ‘yan sanda na musamman sun yi kokarin kubutar da wasu baki da shugaban mazauna gidan yarin ya yi garkuwa da su.

Kungiyar da ke kare hakkin fursunoni a kasar ta ce, fursunonin nada makamai a hannunsu, inda suka harbi jami’an ‘yan sandan, sannan kuma suka tayar da wasu kanana bama-bamai.

Rahoton jami’an ‘yan sanda ya ce, shugaban fursunonin, Wilfredo Ramos na cikin wadanda aka kashe a rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.