Isa ga babban shafi
DR-Congo

Gawar Tshisekedi za ta koma Congo bayan shekaru biyu a Belgium

Iyalan tsohon shugaban 'yan adawan Jamhuriyar Demokiradiyar Congo, Etienne Tshisekedi sun bayyana cewar za a mayar da gawarsa gida daga kasar Belgium shekaru biyu bayan mutuwarsa a can.

Tsohon jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Congo, Etienne Tshisekedi.
Tsohon jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Congo, Etienne Tshisekedi. THIERRY CHARLIER / AFP
Talla

Etienne Tshisekedi wanda shi ne mahaifin shugaba Felix Tshisekedi da aka rantsar a matsayin shugaban kasa a wannan shekara, ya rasu bayan ya gamu da rashin lafiya a Belgium yana da shekaru 84, amma rikicin siyasar kasar ya hana a mayar da gawarsa gida.

Dan uwansa, Arch Bishop Gerard Mulumba ya ce, ranar 30 ga watan nan za a mayar da gawar gida, kana a yi masa jana’iza ranar 1 ga watan Yuni.

Marigayin ya taka rawa a fagen siyasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo duk da cewa, bai samu nasarar zama shugaban kasa ba, yayinda ya kasance kan gana wajen sukar mulkin kama-karya na Mobuto Sese Seko.

Bayan fitowarsa daga gidan yari a shekarar 1982, marigayin ya jagoranci kafa jam'iyyar Union for Democracy and Social Progress, wadda ta zama babbar jam'iyyar adawa a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.