Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta gargadi Amurka kan yi mata barazana

Iran ta gargadi Amurka ta rika girmama kimarta a matsayin kasa mai ‘yanci, tare da kaucewa yi mata barazana.

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif.
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif. REUTERS/David Mdzinarishvili
Talla

Iran ta maida martani ne kan barazanar shugaban Amurka Donald Trump na rusata,muddin ta kaiwa muradunta hari.

Yakin cacar baka tsakanin kasashen biyu na dada zafafa ne bayan da kamfanin dillancin labaran Iran ya sanar da cewa kasar ta kara ninki hudu, na yawan makamashin Uranium da ta ke sarrafawa, a wani mataki na aiwatar da shawarar da ta yanke na janyewa daga wani bangaren yarjejeniyar 2015 da ta cimma da manyan kasashen duniya, kan shirinta na nukiliya.

Trump a shafinsa na Twitter ya yi wa Iran barazanar cewa da rabon karshenta ya gabato da wuri idan har ta ci gaba da takalar yaki da Amurka.

Sai dai ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya ce kasar ta shafe daruruwan shekaru tsakanin abokan gaba, kuma ta fito babu ko kwarzane, saboda haka ta’addancin tattalin arziki da barazanar kare dangi ba zai kawo karshenta ba.

Dangantaka tsakanin Amurka da Iran ta yi tsami a shekarar bara, lokacin da shugaba Donald Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar 2015, wanda ta baiwa Iran din damar samun sa’ida dangane da takunkuman da aka kakaba mata, bayan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.