Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/09 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 13/09 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 13/09 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/09 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 13/09 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 13/09 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/09 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/09 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/09 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/09 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/09 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/09 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 13/09 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 13/09 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/09 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/09 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 13/09 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

An biya ba'amurke diyyar zaman yarin shekaru 45 bisa kuskure

media An daure Philips ne lokacin da yake da shekaru 27 a duniya inda ya shafe shekaru 45 a yari REUTERS

Jihar Michigan da ke kasar Amurka ta biya wani mutum diyyar Dala miliyan daya da rabi saboda wanke shi da kotu ta yi, bayan ya kwashe shekaru 45 a gidan yari akan laifin da bai aikata ba.

Shi dai wannan mutumin da iftilai ya fada akan sa an bayyana sunan sa a matsayin Richard Philips, wanda tsohon ma’aikacin kamfanin hada motoci ne da kotu ta samu da laifin kisan kai a shekarar 1972 a Jihar Michigan da ke Amurka, sakamakon shaidar karya da wani ya bayar.

An daure Philips ne lokacin da ya ke da shekaru 27 a duniya, kuma bayan wani bincike da Jami’ar Michigan ta gudanar, wanda ya bayyana shi a matsayin mutumin da yafi kowa dadewa a gidan yarin Amurka duk da ya ke babu shaidar da ya tabbatar da laifin da ya aikata, matakin ya sa an sallame shi daga gidan yari bara.

Philips wanda yanzu haka ya ke da shekaru 73 a duniya, bayan kwashe shekaru 47 a gidan yari, ya karbi Dala miliyan guda da rabi, tare da wasu irin sa guda biyu da suma aka daure su cikin kuskure.

Sauran mutane biyun sun hada da Neal Redick da ya karbi Dala 780,000 bayan kwashe kusan shekaru 16 a gidan yari saboda zargin lalata da karamar yarinya, da Raymond McCann da ya karbi Dala 40,000 saboda daure shi na shekara guda saboda gabatar da takardun karya.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure