Bakonmu a Yau
Farfesa Muntaka Usman na Jamiar Ahmadu Bello da ke Zaria kan rikici tsakanin Google da Huawei
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:40
Miliyoyin masu amfani da wayoyin hannu na Android a sassan duniya za su fuskanci matsalolin amfani da wayoyin na su saboda matakin da manyan kamfanonin Google na Amurka da kuma Huawei na China suka dauka na yanke dankon zumuncin da ke tsakaninsu.Matakin wanda ke zuwa a wani lokaci da kasashen biyu ke cacar baka da yakin cinikayya tsakanin su.Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Muntaka Usman na Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria masani tattalin arziki na duniya don jin yadda suke kallon lamarin.