Isa ga babban shafi
China-Amurka

China ta sanar da kara kudin haraji zuwa Amurka

A makon da ya gabata, China ta ce, har yanzu tana da aniyar tura tawagarta zuwa Amurka domin tattaunawar kasuwanci da hukumomin Washington, duk da cewa shugaba Donald Trump ya lashi takobin kara kudin haraji kan kayyakin da China ke shigar da su Amurka.Sabon matakin da Amurka ta dau a yau litinin ya sa China sanar da dora sabon haraji a kan kasar Amurka da zai kai dala milyan dubu 60 wanda kuma zai fara aiki daga ranar 1 ga watan yuni mai zuwa,

Wakilan Amurka da China  a zaman tattaunawa dangane da rikicin kasuwanci tsakanin su
Wakilan Amurka da China a zaman tattaunawa dangane da rikicin kasuwanci tsakanin su 路透社
Talla

Shugaba Donald Trump ya kara kudin harajin ne a wani lokacin da aka sa ran kasashen biyu zasu cimma jituwa bayan da wakilan China suka sauka Amurka da kuma bayan sa’o’I biyu suka kama hanyar komawa gida ba tareda samun biyan bukata daga wakilan Amurka.

ake kallo a matsayin wani yunkuri na karshe da zai kai ga cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu ko kuma ta kara farfado da yakin kasuwanci a tsakaninsu.

A Litinin da ta gabata ne, Trump ya kara nanata cewa, suna asarar Dala biliyan 500 a harkar kasuwanci da China, in da ya ce, ba za su sake amincewa da haka ba.

Wannan dai haraji na a matsayin ramuwar gayya da zai kama daga kashi 5 zuwa 25 cikin dari na hajojin da Amurka ke sayar wa China, matakin da ke zuwa kwanaki kadan bayan da Amurka ta lafta wa China irin wannan haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.