Isa ga babban shafi
Venezuela

Amurka na shirin daukar matakin Soji kan Venezuela

Gwamnatin kasar Amurka tace a shirye take ta dauki matakin soji domin kawo karshen rikicin dake gudana a kasar Venezuela sakamakon arangamar da ake tsakanin masu goyan bayan shugaban yan adawa Juan Guaido da kuma jami’an tsaro.

Nicolas Maduro,Shugaban kasar Venezuela
Nicolas Maduro,Shugaban kasar Venezuela REUTERS
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana karara cewar akwai yiwuwar amfani da karfin soji idan bukatar haka ta taso, kuma Amurka za tayi haka.

Pompeo yace fatar Amurka itace ganin an samu mika mulki cikin kwanciyar hankali domin ganin shugaban yan adawa ya karbi ragamar tafiyar da kasar, a shirin da ake yi na gudanar da sabon zabe.

Sakataren yace idan ba’a samu yin haka ba, kuma yanayi ya tabarbare, lallai shugaban kasa zai yanke hukunci akai, kuma zasu aiawatar.

Shi kuwa mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, John Bolton yace yau Pompeo zai tattauna da takwaran sa na Rasha Sergei Lavrov kan halin da ake ciki a kasar ta Venezuela.

Rahotanni sun ce akalla mutane sama da 60 suka samu raunuka jiya.

Bolton yace babu abinda Rasha keyi sai sanya musu yatsa a ido wajen tura sojojin Cuba da kuma mamaye kasa a wannan Yankin, matakin da ya bayyana shi a matsayin tsohon yanayi kuma ba mai dorewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.