Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen duniya 130 na taron sauyin yanayi a Paris

Wakilan kasashen duniya 130 sun soma taron kwanaki biyar a birnin Paris domin nazari kan yanayin gurbacewar muhalli da cimma matsaya kan hanyar magance matsalar, sai kuma ceto halittun da gurbacewar muhallin ke yi wa barazana.

Taron sauyin yanayi a birnin Paris na Faransa
Taron sauyin yanayi a birnin Paris na Faransa REUTERS/Etienne Laurent/Pool
Talla

Wani rahoton masana muhalli mai shafuka 44 ya ce, dan adam na haifar da illoli ga muhallinsa ta hanyoyi sama da dubu daya, kuma kai tsaye matsalar gurbacewar muhallin na tasiri ne kan iskar da muke shaka, ruwan sha mai tsafta, da kuma kasar noma.

A halin da ake ciki kuma, kamar yadda wannan rahoto ya nuna, nau’ikan halittu daban-daban akalla miliyan daya ne ke fuskantar barazanar karewa baki daya daga doron kasa, mafi akasarinsu kuma nan da shekaru kadan duk a dalilin gurbacewar muhallin, wanda masanan suka ce, kashi uku bisa hudu na fadin kasar duniyarmu ya gurbata.

Kwararrun kan muhallin da canjin yanayi, sun kuma yi gargadin cewa, mutuwa ko bacewar kwarin da suke taka muhimmiyar rawa wajen barbara ko auratayya tsakanin tsirrai, musamman Zuma, na barazanar haifar da hasarar amfanin gona da darajarsa za ta kai kimanin dala biliyan 500 a kowace shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.