Saudiya na kashe 'Yan Shi'a a kasar- Amnesty
Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama na duniya da suka hada da Human Rights Watch da Amnesty International sun yi zargin cewar, 33 daga cikin mutane 37 da Saudi Arabia ta aiwatarwa da hukuncin kisa, mabiya akidar Sh'ia ne.
Wallafawa ranar:
Adam Coogle na Kungiyar Human Rights Watch ya yi zargin cewar, shari’ar da aka yi wa wadannan mutane bata da inganci, yayinda Daraktar Amnesty International a Gabas ta Tsakiya, Lynn Maalouf ta ce, wannan ya nuna yadda ake amfani da hukuncin kisa saboda siyasa.
Kakakin Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani ta ce, suna kira ga gwamnatin Saudi Arabia da ta sake duba wadannan shari’u, musamman wasu guda uku daga cikinsu.
Jami'ar ta ce, suna da labarin cewar, wasu daga cikin wadanda aka aiwatar da hukuncin kisan, yara ne kanana 'yan kasa da shekaru 18.
A cewar Shamdasani, dokokin duniya sun haramta kashe kananan yara. yayinda ta ce, rahotannin da suka samu sun nuna musu cewa, wadanda aka kashe sun aikata laifin shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar ne.
Kodayake jami'ar ta ce, hukuncin da aka yanke wa wadannan mutane ya yi daidai da dokar yaki da ta’addanci a Saudiya, amma ta ce, suna kira ga mahukuntan kasar da su sake nazari kan dokar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu