Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/12 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 13/12 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/12 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 13/12 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/12 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/12 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/12 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/12 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/12 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 13/12 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 13/12 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

Saudiya na kashe 'Yan Shi'a a kasar- Amnesty

media Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Saudiya da ta sauya dokokinta na aiwatar da hukuncin kisa IRAQ JUSTICE MINISTER / AFP

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama na duniya da suka hada da Human Rights Watch da Amnesty International sun yi zargin cewar, 33 daga cikin mutane 37 da Saudi Arabia ta aiwatarwa da  hukuncin kisa, mabiya akidar Sh'ia ne.

Adam Coogle na Kungiyar Human Rights Watch ya yi zargin cewar, shari’ar da aka yi wa wadannan mutane bata da inganci, yayinda Daraktar Amnesty International a Gabas ta Tsakiya, Lynn Maalouf ta ce, wannan ya nuna yadda ake amfani da hukuncin kisa saboda siyasa.

Kakakin Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani ta ce, suna  kira ga gwamnatin Saudi Arabia da ta sake duba wadannan shari’u, musamman wasu guda uku daga cikinsu.

Jami'ar ta ce, suna da labarin cewar, wasu daga cikin wadanda aka aiwatar da hukuncin kisan, yara ne kanana 'yan kasa da shekaru 18.

A cewar Shamdasani, dokokin duniya sun haramta kashe kananan yara. yayinda ta ce, rahotannin da suka samu sun nuna musu cewa, wadanda aka kashe sun aikata laifin shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar  ne.

Kodayake jami'ar ta ce, hukuncin da aka yanke wa wadannan mutane ya yi daidai da dokar yaki da ta’addanci a  Saudiya, amma ta ce, suna kira ga mahukuntan kasar da su sake nazari kan dokar.

Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure